Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sake lashe kambin zakarar wasannin firimiya lig na Najeriya a bana, wanda shi ne karo na uku a jere da kungiyar take yin irin wannan bajimta.
Duk da cewa akwai sauran mako guda kafin a zo ga karshen kakar kwallo ta bana a Najeriya, Kano Pillars ta yi fintinkau ma kungiyar dake hankoron wannan kambi, watau Enyimba wadda a karshen mako ta yi kunnen doki da ci 1 da 1 da Dolphins a Port Harcourt. Wannan yana nufin cewa maki 65 da Pillars ke da shi, babu mai iya samu a duk cikin sauran kungiyoyin da suke hankoron kambin.
Kano Pillars zata wakilci Najeriya a gasar Lig ta Zakarun Kulob ta Nahiyar Afirka a shekara mai zuwa, tare da duk kungiyar da zata zo ta biyu a Firimiya Lig.
Kungiya ta uku kuma, ita ce zata wakilci Najeriya a gasar kofin Confederation ta Afirka ta 2015. Wadanda suke hankoron wannan kambi kuwa a yanzu sune Warri Wolves, Nassarawa United da kuma Ahbia Warriors.