Janar Gowon ya shaida hakan ne, a hira da yayi da manema labarai a garin Gombe, a taron neman zaman lafiya wanda hukumar bunkasa kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, tare da hadin gwiwar wasu hukumomin gwamnatin Tarayya.
“Wadannan yara, muna rokonsu, don Allah, su duba abunda sukeyi, su bamu zama lafiya a kasarnan. Idan suna so ne, mu hadu dasu mu tattauna, zan so mu sadu da su,” a cewar Janar Gowon.
Farfesa Muhammad Al-amin ya gabatar da kasida dake karin haske akan abubuwan dake jawo kungiyoyi masu tayar da kayar baya “duk inda ya zamo ba’a shugabanci na adalci, duk inda ya zama dukiyar kasa bata zagayawa, duk inda ya zamo, malaman addini an barsu kara zube, hakan na bada jagoranci har ta kaiga tsageranci.
Har yanzu ‘yan bindiga da ake kira Boko Haram na cigaba da addabar arewa maso gabashin Najeriya, ta kashe jama’a, garkuwa da jama’a, kona garuruwa da kame kauyuka.
Your browser doesn’t support HTML5