Za'a Binne Dr. Sheikh Umar Khan Kamar Yadda ake Binne Sauran Masu Ebola

Ma'aikatan kiwon lafiya na kungiyar MSF su na shirin kai abinci ma masu fama da Ebola da ake kebe a wani asibitin da kungiyar ta bude don kula da masu Ebola a Kailahun a kasar Saliyo

Liberiya ta ce zata sanya 'yan sanda su na yin rakiya ma ma'aikatan kiwon lafiya, a bayan da aka kai farmaki kan wasunsu lokacin da suke kula da wadanda suka kamu da cutar Ebola, ko kuma kokarin binne wadanda cutar ta kashe.

Wannan yana daya daga cikin matakan da gwamnatin Liberiya ta dauka yau laraba yayin da kasashen Afirka ta Yamma suke kai gwauro da mari da nufin shawo kan barkewar annoba mafi muni ta cutar Ebola da aka taba gani.

Ya zuwa yanzu mutane kimanin 700 ne suka mutu daga wannan cuta a kasashe 7 a yankin.

A Saliyo, inda babban likita mai yaki da cutar Ebola ya mutu jiya talata a sanadin wannan cuta da yake kokarin yaka, gwamnati ta ce za a binne Dr. Sheikh Umar Khan, a bisa ka'idoji masu tsauri da aka shimfida na binne mutanen da cutar Ebola ta kashe.

babu allurar rigakafi ko kuma maganin warkar da cutar Ebola, wadda take haddasa zazzabi, da amai ko haraswa, da gudawa, da ciwon jiki, sai kuma yoyon jini ta wurare kamar ido, kunne da hanci.