Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Killace Asibitin Da Wani Mai Fama Da Ebola Ya Mutu A Ciki A Lagos


ma'aikatan lafiya su na daukar jini a jikin wata mace mai fama da cutar Ebola
ma'aikatan lafiya su na daukar jini a jikin wata mace mai fama da cutar Ebola

Najeriya ta rufe ta kuma killace wani asibitin dake Lagos, inda mutumin farko da aka samu da cutar Ebola a Najeriya ya mutu a makon da ya shige.

Wannan matakin da Najeriya ta dauka a yau litinin, yana zuwa ne a yayin da kasashen Afirka ta Yamma suke kokarin dakile yaduwar kwayar cutar ta Ebola, wadda ya zuwa ta kashe mutane kusan 700 a yankin.

Jiya lahadi, Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce zata tura kwararrun masana kan yaduwar cututtuka zuwa Najeriya da Togo, domin bin sawun mutanen da suka yi hulda ko cudanya da ma'aikacin gwamnatin kasar Liberiya wanda ya je Lagos a jirgin sama ranar 20 ga watan Yuli, ya kuma mutu kwanaki biyar bayan isarsa.

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Liberiya ta ce zata rufe akasarin bakin iyakokin kasarta domin hana bazuwar kwayar cutar.

Amma kuma za a bar babban filin jirgin saman Monrovia da wani na lardi da kuma wasu iyakokin kasa guda uku a bude, sai dai za a dauki kwararan matakan rigakafi a wadannan wuraren.

Har ila yau, gwamnatin ta haramta yin taron jama'a, ciki har da bukukuwa da zanga-zanga.

XS
SM
MD
LG