Majalisar Dokokin Najeriya ta Baiwa Kwamitin Dake Kula da Harkokin Shige da Fice Mako Daya

Masu neman aiki sun shiga fafitikar neman aiki da Hukumar Shige da Fici a Abuja ranar 15 ga watan Maris shekarar 2014.

Majalisar Dokokin Najeriya ta Baiwa Kwamitin Dake Kula da Harkokin Shige da Fice Mako Daya
Majalisar,dokokin Najeriya ta baiwa kwamitin dake kula da harkokin shige da fice, mako daya da ta yin bincike kuma ta bada rahoto akan shirin da aka gudanar na jarabawa na masu neman aikin shige da fice.

Mutane goma sha tara ne suka rasa rayukansu,takwas a Abuja, uku a Minna, biyar a Port Harcourt da kuma uku a Benin babban birni jihar Edo.

Shima shugaban, kungiyar kwadago na kasa Abdulwaheed Umar, yayi Allah wadai da yanda hukumar shige da fice ta kudanar da wanna jarabawa.

Inda yake cewa wanna shirin kusa da gangar aka shirya domin dan abinda za a samu.

-2' 52"