Har yanzu Da Sauran Aiki Kan Yaki Da Polio - Dr. Hajo Sani

Tarukkan inganta kiyon lafiya na gidan rediyon murkyar Amurka (VOA) a biranen kaduna da Minna na Nigeria

Tsohuwar ministar harkokin matar a Najeriya ta ce tilas a daura damarar kara wayarwa da jama'a kai dpomin su fahimci dimbin amfanin rigakafin cutar ta Polio
Wata kungiya ta tallafawa kula da lafiyar iyali, ta ce da sauran aiki a gaba ganin yadda har yanzu jama'a suke jahiltar kokarin da ake yi na kawar da cutar shan inna, Polio, daga doron kasa.

Daga cikin kasashe fiye da 120 da aka kaddamar da shirin kawar da wannan cuta a cikinsu dai, an samu nasarar kawar da ita a kusan dukkansu, im ban da Najeriya da Pakistan da Afghanistan kawai.

Daya daga cikin darektocin Kungiyar "Society For family Health" Dr. Hajo Sani, wadda tsohuwar minista mai kula da harkokin mata ce, ta ce abin takaici shi ne akwai masana wadanda da gangan suke kara janyo rudani tsakanin jama'a game da wannan aikin.

Tana magana ne a Minna, Jihar Neja, daya daga cikin jihohyin da suka lashe kyautar yabo ta Gidauniyar Bill Gates a saboda gagarumin kokarin da suka yi wajen kawar da wannan cuta.

Shi ma gwamna Babangida Aliyu, yayi jawabi.

Ga Mustapha Nasiru batsari, da cikakken bayanin wannan yunkurin.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Mustapha Nasiru Batsari Kan Polio Daga Neja - 3:39