Ana Mayarda Martani Game Da Kiran Cewa A Kama Muhammadu Buhari

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya

Kiran da Pasto Ayo Oritsejafor yayi na a kama Muhammadu Buhari ya koma dambarwa a tsakanin 'yan siyasar dake ci gaba da maida martani daga bangaren gwamnati da na hamayya
Kiran nan da shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya, Pasto Ayo Oritsejafor, yayi na cewa a kama Janar Muhammadu Buhari, ya koma dambarwa tsakanin 'yan siyasar dake kiraye-kiraye bisa alkiblar jam'iyyun da suke wakilta.

A bayan da janar Buhari ya bayyana yanayin aiwatar da dokar-ta-bacin da gwamnatin tarayya ta kafa a zaman yaki kan 'yan arewa, da kuma kiran da yayi cewa shugaba Goodluck Jonathan yayi murabus domin ya gaza, sai Pasto Oritsejafor, ya fito yana kiran da a kama Buhari a gurfanar da shi gaban kotu.

Sai dai kuma da yake mayarda martani kan wannan furucin, sakataren jam'iyyar CPC ta kasa, Malam Buba Galadima, yayi kashedin cewa a guji lakace musu hanci, yana mai fadin cewa irin wadannan kalamu ba su cancanci fitowa daga bakin shugaban addini ba, domin ta 'yan siyasa ce.

Buba Galadima yace Janar Buhari yayi magana don kishin kasarssa ce.

Shi ma wani shugaban matasan jam'iyyar PDP mai mulki, Ado Buni Yadi, yace irin wadannan kalamun, gafaka ce ta 'yan siyasa, ba ta shugabannin addini ba, na Kirista ko na Musulunci.

ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa, Nasiru Adamu el-Hikaya, ya aiko daga Abuja kan wannan batun...

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya Na Martani Game Da Kiran A Kama Buhari - 3'13"