A Hada Malamai A Zaure Guda Su Tattauna Cutar Polio

Shugaban kungiyar masu fama da cutar Polio tare da sauransu a Kaduna sun ce hada malaman suyi muhawara ne zai kawo fahimta kan rigakafinta
An bukaci hukumomi da sauran masu hannu a gwagwarmayar da ake yi ta kawar da cutar shan inna, ko Polio, daga doron kasa, musamman ma a Najeriya, da su hada malamai masu goyon baya da wadanda suke yin adawa da rigakafin cutar a zaure guda, domin su yi muhawara kan wannan batu.

Ta yin hakan, za a iya samun fahimta tare da cimma matsaya guda wadda zata taimaka a yunkurin kawar da wannan cuta mai nakkasa wadanda suka kamu da ita, ko kuma ma ta kashe su idan ta yi tsanani.

Shugaban Kungiyar Masu dauke da Cutar Polio a jihar Kaduna, Rilwanu Mohammed Abdullahi, yana daga cikin wadanda suka bayyana irin wannan ra'ayin a taron yaki da cutar Polio da Muryar Amurka ta shirya kwanakin baya a garin Kaduna.

Shi ma Luka Maigadi Kajuru, yace sanya ire-irensu masu dauke da wannan cuta a cikin gamgamin yaki da ita, zai sa a kara azamar yakarta a saboda sun san zafinta kuma zasu iya bayyanawa jama'a zahirin illar da wannan cuta ta yi musu.

Your browser doesn’t support HTML5

Rilwanu Mohammed Abdullahi da Luka Maigadi Kajuru Su Na Magana Kan Polio - 3:09