Zazzabin cizon sauro ke da alhakin mutuwar kimanin kananan yara 3000 kowacce rana, da matsaloli masu yawa ga mata masu ciki da ‘ya’yansu, yana kuma sa ciwon kwakwalwa wanda ke rage basira.
Duk da yawan maganin malariya a Nigeria, ta zama cuta ta daya da ke kisa a kasar, bayan cutar sida wato- HIV/AIDS da cutar bugun jini. Yara kasa da shekara biyar da mata masu ciki sune kashi 85 na wadanda ke mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar. Rayuwar wannan yaran da mata masu ciki na da damuwa, duk da kokarin gwamnati da kungiyoyi daban-daban.
Kamfanin Mortein mai sarrafa maganin sauro, na Reckitt Benckiser, a kokarinsu na yaki da cutar cizon sauro, yayinda kuma ake bukin ranar malariya ta duniya (WMD), sun gudanar da ayyukansu a jihar legas tare da goyon bayan ma’aikatar kare cutar malariya, masu aikin jinya, unguwar zoma da ma’aikatan asibitoci na jihohi biyar - Ifako-Ijaiye, Gbagada, Lagos Island, Ajeromi-Ifelodun da Surulere; da kuma shugabannin kananan hukumomi, sunyi kokarin yiwa mutane jawabi kan abinda ke kawo cutar malariya da maganin ta.
Lokacin da yake Magana a taron, zaunannen sakatare na karamar hukumar Ifako-Ijaiye, Olufemi Olugbile, da ya wakilci kwamishinan lafiya, yayi kira ga mazauna gari da su tsabtace muhallansu ta wurin share magudanar ruwa da hanyoyin ruwa, musamman lokacin damina, saboda kada sauro su hayayyafa. Ya basu tabbacin cewa gwamnati zata kara maida hankali a fannin lafiya domin kiyaye cututtuka da rage yawan mace-mace.
Shima, directan ciniki na Reckitt Benckiser, Sanjay Kashyap yace kamfanin Mortein ya hada gwiwa da ‘yan kasuwa a kokarinsu na aiwatar da shirin lafiya, da kauda matsalar cutar malariya.
Wakilan Reckitt Benckiser sun bayyana mahimancin wannan yakin da karfafa mata masu shayarwa inda ake koya musu yadda zasu kiyaye kansu, ‘ya’yansu da iyalansu daga mutuwar da malariya ke kawowa.