Mutane Miliyan Daya Suke Dauke Da Kwayar Cutar HIV a Jihar Binuwe

Ana gwada jinin mutane domin tabbatar da masu dauke da cutar HIV

Kwamitin yaki da cutar kanjamau na jihar Binuwe ya bayyana cewa, kimanin mutane miliyan daya ke dauke da cutar a jihar.

Babbar sakatariyar kwamitin Ashi Wende ce ta bayyana haka a wajen wani taron karawa juna sani da aka shiryawa manema labarai kan yaki da cutar kanjamau. Bisa ga cewarta, wadanda suke dauke da cutar sun hada da kananan yara sama da dubu dari uku wadanda suke bukatar maganin kashe kaifin cutar.

Mrs Wende tace, sama da mutane dubu ishirin da daya da suke dauke da cutar, mutane ne da basu dade da kamuwa da ita ba, daga cikinsu kuma sama da dubu goma sha bakwai mata ne.

Shugabar kwamitin yaki da cutar kanjamau ta jihar Binuwe tace gwamnatin jihar ta samar da cibiyoyin shan magani arba’in domin shawo kan yaduwar cutar.

Da wannan yunkurin, jihar Binuwe tafi kowacce jiha a Najeriya yawan cibiyoyin kula da masu dauke da cutar HIV, ta kuma samar da isasshen maganin da za a rika ba wadanda suke dauke da cutar da zai kai har zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, shekarar da aka kaddaye domin shawo kan cutar a duniya baki daya karkashin shirin muradin karni.