'Yan sandan tarayya da na Boston duk sun musanta rahotannin cewa an kama wani mutum dangane da harin bam na Boston
WASHINGTON, DC —
Hukumomin tabbatar da bin doka na Amurka sun musanta rahotannin da kafofin labarai ke yadawa cewa an kama wani mutumin da ake zargi da hannu a hare-haren bam guda biyu ranar litinin a lokacin tseren famfalaki na Boston.
Hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, FBI, da masu gabatar da kara na tarayya da kuma rundunar 'yan sandan birnin Boston, duk sun fito ayau laraba su na musanta rahotannin da gidajen telebijin da rediyo har ma da jaridu suke bugawa cewa an kama mutum.
Masu bincike sun fadawa kamfanonin dillancin labarai cewa wata kyamara ta bidiyo daga wani kanti dake kusa, ya nuna wani mutumi ya dauko wata bakar jaka, kuma a bisa dukkan alamu sai ya ajiye ta a kusa da inda daya daga cikin tagwayen bama-baman ya tashi ya kashe mutane uku, ya raunata wasu 176.
Gidan telebijin na CNN yace wani kanti dake kusa da nan ya dauki bidiyo mai matukar muhimmanci na wani mutumi dauke da bakar jaka, haka kuma hotunan bidiyon da wani gidan telebijin na Boston ya dauka a wurin shi ma ya taimaka ainun wajen bins awun mutumin don ganin take-takensa a wurin.
nan da awa daya ake sa ran hukumomi zasu gudanar da taron 'yan jarida domin yin karin haske game da yadda bincikensu ke gudana.