Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Abubuwa Sun Yi Bindiga A Boston


rahotanni na baya baya sun ce mutane 2 sun mutu, wasu 23 kuma sun ji rauni a fashe-fashen da ba a san musabbabinsu ba har yanzu

Mutane akalla 6 sun ji rauni a lokacin da wasu abubuwa guda biyu suka yi bindiga a kusa da inda ake kammala gudun famfalaki na shekara da aka saba yi a birnin Boston dake Jihar MA a nan Amurka yau litinin.

Hotunan bidiyo a telebijin sun nuna inda wurin ya hargitse, ga tarkace da jini ga kuma ma’aikatan jinya na gaggawa dauke da gadajen jigilar marasa lafiya.

An yi ta daukar ‘yan kallo jina-jina zuwa tantin da aka kakkafa domin kula da ‘yan gudun da watakila zasu gaji ko zasu samu wata matsala. ‘yan sanda sun yi ta kutsawa cikin maguda a lokacin da suka juya da baya zasu koma titunan da suka biyo lokacin gudun.

Wata mai magana da yawun babban asibitin MA ta ce su na jinyar mutane 4 a asibitinsu. Har zuwa yanzu, jami’an dake shirya wannan gudu na famfalaki ko na gwamnati ba su fito sun yi kiyasin adadin mutanen da suka ji rauni ko kuma irin tsananin raunin da suka samu ba.

Wadannan abubuwa biyu sun fashe jim kadan a bayan da maguda na farko daga cikin mutane dubu 27 da suka shiga wannan gudun famfalaki suka fara kammala gudun nasu. An dakatar da wannan tsere a bayan fashewar abubuwan guda biyu, aka kuma dakatar da zirga zirgar jiragen karkashin kasa masu bi ta yankin.

Wata mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin NY ta ce sun kara daukar matakan tsaro a muhimman wurare na birnin a bayan wannan abu da ya faru a Boston.

Birnin Boston dai na daya daga cikin manyan biranen kasar nan, kuma yana yankin arewa maso gabas. Wannan gudun famfalaki na Boston muhimmin tsere ne dake samun halartar maguda daga ko ina a duniya, wanda kuma ake gudanarwa kowace shekara.
XS
SM
MD
LG