Mutane 3 Sun Mutu, 140 Sun Ji Rauni A Boston

Shugaba Obama kennan da yake magana da manema labarai dangane da harin birnin Boston.

Hukumomin tarayya na Amurka sun binciki wani gida dake unguwar Rivera ta birnin Boston a ci gaba da suke da kokarin farauto wa’anda suka cinna ta’asar girka bama-bamman da suka tashi jiya a birnin a lokacin gudun fanfalaki, inda har mutane 3 suka rasa rayukkansu, wasu 140 suka ji rauni.
WASHINGTON, D.C - An ga jami’an tsaro suna ta zaro kayyayaki iri-iri, suna ficewa da su daga gidan, amma har yanzu ba wanda aka kama, kuma hukumomi sun kama bakinsu sun tsuke akan wanda suke zaton sun aikata wannan danyen aikin.

Yanzu fa dai Hukumar yaki da manyan laifukka ta Amurka, FBI ce take wa sauran bangarorin ma’aikatu jagorancin gudanar da binciken wannan al’amarin da yanzu fadar White House ta shugaban Amurka take kira “aikin ta’addanci.”

Har zuwa yanzu ba wani mutum ko kungiya da suka fito suka dauki alhakin kawo wannan farmakin to amma shugaba Barack Obama na Amurka yace ko su waye, za’a gano su, kuma zasu fuskanci shara’a:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Obama yana magana akan harin Boston


Yace: Har yanzu bamu san ko waye ya aikata wannan ko dalinsu ba, kuma bai kamata mu yanke hukunci kafin mu san gaskiyar abinda ya faru ba, amma fa a tabatta: sai mun gano bakin zaren! Zamu gano ko waye ya aikata wannan, zamu gano dalilinsa, kuma kowane mutum ko kungiya ce, zamu kama su da laifin.”