Dakarun JTF Sun Kashe Mutane 14 A Jihar Rivers

Sojojin Najeriya su an duba wata motar da aka kai harin bam da ita.

A bayan da dakarun na JTF suka kashe mutane fiye da 40, akasarinsu matasa, a garin Maidugurin Jihar Borno a ranar alhamis
Dakarun tsaron Najeriya sun kashe wasu mutane 14, a lokacin da suka kai sumame a wata maboyar gungun wadanda suka sace wani mutumi dan kasar Turkiyya.

‘Yan sanda sun ce an kai wannan sumame jiya jumma’a a Jihar Rivers mai arzikin man fetrur. Jami’ai suka ce tsageran yankin su na da hannu a wasu sace-sacen mutane, da fashi da makami da wasu tashe-tashen hankula.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace an sako mutumin dan kasar Turkiyya da aka sace a bayan da aka biya mutanen da suka sace shi kudin fansa.

A wani lamarin dabam da ya faru ranar alhamis, shaidu sun ce sojoji sun bindige suka kashe mutane fiye da arba’in, akasarinsu matasa, a garin Maiduguri.

Mazauna wannan gari inda kungiyar nan ta Boko Haram ta fi karfi, sun ce sojoji daga rundunar nan ta hadin guiwa da ake kira JTF, sune suka karkashe wadannan mutane a lokacin da suka kai sumame a unguwanni da dama na garin da maraicen alhamis.

Wani ma’aikaci a dakin ajiye gawarwaki a birnin ya shaidawa VOA cewa sun shigo aiki jiya jumma’a da safe sai suka samu gawarwakin matasa kimanin 40 sojoji sun jibge musu a wurin.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na Amnesty International da HRW sun zargi rundunar JTF da laifin kashe mutane haka siddan a kokarinta na murkushe ‘yan Boko Haram. Rundunar ta JTF ta musanta wannan zargi.