Rumbun Hotuna Jana'izar Mutanen Da Aka Kashe A Madalla 00:00 Fabrairu 02, 2012 Mata kenan ke kuka a yayin jana’izar bai daya ta wadanda su ka rasu a harin bam din ranar Kirsimeti a majami’ar Katolika ta St. Theresa. Limaman coci kenan ke jagorantar addu’o’i yayin jana’izar wadanda aka kashe a harin bam din na Madalla. Jama’a na kallo a yayin da ‘yan kungiyar agajin Boys Scouts ke dauke da akwatunan gawarwakin wadanda aka kashe a harin. Limaman coci kenan a harabar makabartar wadanda aka kashe a harin. Wasu mata kenan ke nuna alhini a lokacin jana’izar bai daya ta wadanda su ka rasu a harin bam din ranar Kirsimeti a majami’ar Katolika ta St. Theresa. Wata mace kenan ke ta kuka a yayin jana’izar bai daya ta wadanda su ka rasu a harin bam din ranar Kirsimeti a majami’ar Katolika ta St. Theresa din. An Yi Jana'izar Wadanda Harin Ranar Kirsimeti A Unguwar Madalla Ya Rutsa Da Su