Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zlatan Ibrahimovic Ya Sami Karin Albashi Kimanin Naira Miliyan 420 A Kowane Wata


Kungiyar kwallon kafa ta P S G ta yi ma zakaran dan wasanta Zlatan Ibrahimovic karin tsabar kudi har dala dubu 760 a kowane wata, watau karin kusan Naira miliyan dari 200 a kowane wata, abinda ya sa ya zamo a yanzu babu wani dan kwallon kafar dake samun albashi mai tsokar nasa a kasar Faransa.

A yanzu Ibrahimovic zai rika samun albashin Dala miliyan daya da dubu 635 a kowane wata, watau kimanin Naira miliyan 420 kowane wata ke nan, karkashin wannan kwantaragi nasa. Ibrahimovic dan kasar Sweden, kuma mai shekaru 34 da haihuwa, ya koma kungiyar ta PSG daga AC Milan a shekarar 2012, kuma a cikin wasanni 156 da ya buga mata, ya jefa kwallaye har 127.

A bayan wannan kudin kuma, Ibrahimovic zai iya samun tukuici mai tsoka har kala uku idan kungiyar PSG ta lashe kofin zakarun kulob kulob na Turai, ko ta lashe wasannin lig-lig na Faransa, ko kuma idan aka kammala kakar kwallon bana yana matsayin wanda ya fi kowa jefa kwallo da bayar da kwallo ma wani ya jefa.

Wannan tukuici na biyun kusan kamar ya same shi za a ce domin kuwa a yanzu haka PSG ce take saman teburin lig na Faransa, yayin da kungiyar dake bi mata, take can baya da ratar maki 21 a tsakaninsu. A wasannin cin kofin zakarun kulob kulob na Turai kuwa, PSG zata kara da Chelsea ta Ingila a wata mai zuwa a zagaye na biyu na wasannin.

Sai dai kuma jaridar Le parisien da ta fara bada wannan labarin ta ce babu tabbas ko Ibrahimovic zai ci gaba da zama a kungiyar ta PSG a bayan kwantaraginsa na yanzu ya kare a karszhen kakar kwallo ta bana.

Shi dai ya fito da bakinsa yace bashi da niyyar barin kulob din, inda yace dangantakarsa da PSG ta kut da kut ce.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG