Najeriya da kasar Indiya sun jaddada aniyar gina kwakkwarar alaka, inda suka sha alwashin karfafa dangantaka a muhimman fannoni irinsu bunkasa tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da kuma samun wadatar abinci.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar a Abuja a yau Lahadi yayin kammala ziyarar aikin Fira Ministan Indiya, Narendra Modi, ya kawo Najeriya a bisa gayyatar Shugaba Tinubu.
A yayin tattaunawar tasu, shugabannin 2 sun amince da samun karin hadin gwiwa a fannin yaki da ta'addanci da tsaron teku da kuma musayar bayanan sirri.
Fira Minista Modi ya jaddada aniyar Indiya ta tallafawa kokarin Najeriya na zamanantar da harkar tsaronta, inda ya yi karin haske a kan yadda Indiya ta zamo amintacciyar kasa mai kera makamai.
Haka kuma, kasashen 2 sun yi tsokaci a kan kyakkyawar alakar tattalin arzikin dake tsakanin Indiya da Najeriya, inda Indiya ta zamo mafi girman abokiyar kasuwancin Najeriya kuma wacce ke bada muhimmiyar gudunmowa ga bunkasar tattalin arzikinta.
Dandalin Mu Tattauna