Kungiyoyi masu goyon bayan kaurar jama'a daga kasa zuwa kasa, sun gudanar da jerin zanga-zanga a fadin Amurka jiya asabar, domin nuna bacin ransu kan manufofin Shugaba Donald Trump na babu sani ba sabo game da bakin haure.
An gudanar da wannan zanga-zangar a manyan biranen da su ka hada da Washington DC, da Los Angeles. da Houton, da New York da kuma sauran kanana garuruwa a fadin kasar tare da tallfin kudi da kuma goyon bayan kungiyoyi da dama da suka suka hada da kungiyar American Civil Liberty da MoveOn.Org.