Jagoran Addini a Iran ya goyi bayan matakin gwamnatin kasar na kara farashin man fetur a jiya Lahadi, lamarin da ya haifar da mummunar zanga-zanga a karshen mako.
Ayatollah Ali Khamenei ya zargi bata-gari da lalata kayayyaki a zanga-zangar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 2. Kalaman na sa sun zo ne a daidai sa’adda gwamnatin ta rufe yanar gizo a duk fadin kasar ta Iran, a kokarin dakile zanga-zanga a kan karin farashin man da gwamnatin ta yi da kashi 50 bisa 100.
A wani jawabi da yayi wa kasar ta talabijin, Khamenei ya ce wasu sun rasa rayukan su, amma bai yi cikakken bayani ba. Haka kuma ya umarci jami’an tsaro da su gudanar da aikin su.
Bayan jawabin nasa, ma’aikatar binciken asirin kasar, ta ce an gano manyan wadanda suka kitsa tarzomar, kuma ana ci gaba da daukar matakin da ya dace.
Zanga-zangar ta haifar da matsin lamba ga gwamnatin kasar ta Iran, a yayin da take fama da takunkumin kasar Amurka da ke dada tauye kasar, bayan da shugaba Donald Trump ya fitar da Amurka daga yarjejeniyar makamin nukiliyar Iran da manyan kasashen duniya.
Facebook Forum