Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zambia Ta Samu Sabon Shugaban Kasa


Shugaba Edgar Lungu, a dama yayin da ake rantsar dashi
Shugaba Edgar Lungu, a dama yayin da ake rantsar dashi

Edgar Lungu ya maye gurbin shugaban Zambia Michael Sata wanda ya rasu bara

An rantsar da Edgar Lungu a matsayin shugaban kasar Zambia na shida bayan ya ci zabe da ‘yar tazara kadan. To amma abokin hamayyarsa yaki ya amince da sakamakon.

Hukumar zaben kasar tace Mr. Lungu na jam’iyyar Patriotic Front ya samu kashi 48.3 nakuri’un da aka kada. Abokin hamayyarsa Hakainde Hichilema na jam’iyyar United Party for National Development shi ya zo na biyu da kashi 46.7.

To saidai shi Hichilema yace zaben da aka kamala ranar Asabar tamkar an yi masa sata ne domin ba abun da ‘yan Zambia suka zaba ke nan ba.

Yin zaben shugaban kasa ya zama wajibi ne domin rasuwar tsohon shugaban kasar Michael Sata a watan Oktoba din bara. Shi Mr. Lungu zai karkare wa’adin Mr. Sata kafin a yi wani zaben shekara mai zuwa.

Mr. Lungu wanda yayi aiki a ma’aikatar shari’a yace zai kamala ayyukan gina tattalin arzikin kasar da Mr. Sata ya fara.

Masu kada kuri’u basu fito sosai ba kamar yadda aka yi zato sabili da rashin yanayi mai kyau a ranar zaben. To amma masu sa ido a zaben sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an yi zaben da adalci.

Mataimakin shugaba Sata wato Guy Scott shi ya zama mukaddashin shugaban kasar tun mutuwar Mr. Sata. Bisa ga dokar Zambia Mr. Scott bai cancanta ya tsaya takarar shugaban kasa ba domin ba’a haifi iyayensa a Zambia ba. Duk iyayensa ‘yan kasar Scotland ne.

XS
SM
MD
LG