An sako wata jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da aka sace a babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.
Majalisar Dinkin Duniya da Jami’an gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sunce an sako matar ne Jiya Talata bayan sace ta da akayi kuma ake zargin ‘yan bindiga masu alaqa da mayakan anti-Balaka a babban birnin Bangui da aikatawa. Jami’ai sunce matar na aiki ne da ofishin wanzar da zaman lafiya na majalisar da aka fi sani da MINUSCA.
Shekaran jiya Litnin ne matar ‘yar asalin Faransa da wani mutum dake aiki da ma’aikatan agaji na darikar Catholica aka sace su a birnin Bangui.
Sace mutanen biyu yazo ne kwanaki kadan bayan kame wani babban mayakin anti-Balaka da aka fi sani da Janar And-jilo ana zarginsa da laifukan kisa, da tawaye da fyade da kuma sace-sacen kayan jama’a.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada labarin cewa ‘yan tawayen sun bukaci a sake shi, don suyi musaya da Faransawan biyu.
Kasar Jamhuriyar Demokradiyar Kwango ta dade tana fama da tashe-tashen hankula tun shekara ta 2013 lokacin da mayakan Seleka suka hambare gwamnatin Francois Bozize, bisa zargin cewa gwamnatin na cin mutucin Musulmai a arewa maso gabashin kasar.
Laifukan cin zarafin bil adama da mayakan Seleka suka tafka ne yayi dalilin samar da kungiyar mayakan anti-Balaka, lamarin da ya jawo tashe-tashen hankula masu nasaba da bangaranci har ma dubban fararen hula suka tsere zuwa kasashen dake makwabtaka da kasar.
Kasar Faransa ta girke sojoji a kasar, sannan itama kungiyar Kasashen Afirka ta aika sojoji domin dakile tashe-tashen hankula da tarzoma.
SAUTI: Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango Ta Sako Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya - 0" http://bit.ly/1ukeYOJ
HOTO: Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango Lawrence Kabila
#Hausa #Congo DRC