Sardauna ya bar duniya shekaru 50 da suka wuce, amma har yanzu daga shugabannin har talakawa sun kasa mantawa da Sardauna, wanda aka yiwa kisan gillar da aka yi musu tare da su Firayim-Minista Abubakar Tafawa Balewa a lokacin juyin mulkin soji na farko a Najeriya.
Kadan daga ayyukan da Sardauna ya assasa shine inganta ilmin 'yan Arewacin Najeriya da aka barsu a baya, sannan baya la'akari da maganar kabilarka ko addininka matukar kai dan Arewa ne to kana cikin jama'ar da ka cancanci taimakon gwamnatinsa.
Hasalima dai, yawancin gine-ginen ma'aikatun gwamnatin da ke jihohin Arewa musamman Kaduna inda nan ce shelkwatarta, da ka bincika sai ka ji ance Sardauna ya gina. Ya yi asibitoci da makarantu ciki har da daya daga manyan Jami'o'in dake Afirka wato Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kadunan Najeriya.
Matasa sun Muryar Amurka ra'ayinsu na yadda suke jin takaicin yadda Sardauna ya gina Arewa da 'yan Arewa, amma kash! sai gashi su kuma 'yan Arewa kullum sai taron tunawa da Sardauna da karairayin koyi da halinsa amma har yanzu an kasa samun wani Sardaunan a cikinsu.
Karshe ma dai matasan suna ganin ya kamata a daina yin bikin tunawa da Sardauna ta hanyar kade-kade, kamata yayi a dinga tunawa da Sardauna ta hanyar yi masa zaman makokin tunawa da rashinsa. Musamman yadda a shekaru 50 aka kasa cike gibin Gamji dan Kwarai kamar yadda ake mata take.