Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaikayi Ya Koma Kan Mashekiya


Hoton agoguna da wayoyi na hada bama-bamai.
Hoton agoguna da wayoyi na hada bama-bamai.

Bam ya rutsa da wanda ya je dasashi a wani filin wasan kwallon kafa awni fili kusaa da wata makaranta a garin Fotiskum dake jihar Yobe

Yayin da ake shirin bikin Kirsimati rundunar sojoji dake kula da jihohin Borno ,Yobe da Adamawa ta fitar da wata sanarwa inda ta takaita zirga-zirgan ababen hawa a jihohin uku sabili da dalilan tsaro.

Yau mahukuntan suka tsayar zasu bar walwalar mutane da ababen hawa kamar yadda aka saba to amma sai gashi ba zato ba tsammani bam ya sake fashewa a garin Fotiskum cikin jihar Yobe..

Kamar yadda wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya shaida a zantawar da yayi da abokin aiki Aliyu Mustaphan Sokoto bam din ya fashe ne a hannun wanda ya kai ya dasashi a wani babban filin kwallo kusa da wata makaranta inda aka shirya za'a yi wasa yau.Ya kai bam din ne da misalin karfe uku na dare domin ya dasa to amma sai bam din ya tashe. Nan take ya rigamu gidan gaskiya.

Karar fashewar bam din ta razana kowa a garin. Mutane sun ki fitowa daga gidajensu. Kowa ya zauna gida domin tsoron abun da ka iya faruwa musamman yadda jami'an tsaro suka yi ca domin dakile wani tashin hankalin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:50 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG