Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Shugaban Kasar Somalia Yana Karo da Cin Hanci da Rashawa


Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamoud mai ci yanzu wanda yake neman a sake zabarsa karo na biyu
Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamoud mai ci yanzu wanda yake neman a sake zabarsa karo na biyu

Masu sa ido kan shirye-shiryen gudanar da zaben Somaliya, sun ce rashawa tayi katutu a harkar, gabanin zaben Shugaban kasar da za a gudanar gobe Laraba, ta yadda 'yan takara ke ta bai wa 'yan majalisa kyaututtuka da makudan kudade don su samu kuru'unsu.

'Yan takara 23 ne ke kalubalantar Shugaba mai ci Hassan Sheikh Mohmud, wanda ke neman wa'adi na biyu mai tsawon shekaru hudu a matsayin Shugaban wannan kasa ta kuryar Afirka. 'Yan Majalisa, wadanda aka zaba bara, su ne za su zabi Shugaban kasar.

Da ya ke jawabi ga manema labarai jiya Litini, Ciyaman din Kwamitin Yaki da Cin Hanci Mai Zaman Kansa, ya yi barazanar bayyana masu bayarwa da kuma karbar rashawar.

"Mun san abin da ke faruwa a birnin kuma mu na so mu tabbatar cewa komai ya gudana cikin gaskiya kuma bisa doka," a cewar Abdi Ismail Samatar.

Kwamitin, wanda bai da ikon hana komai domin Majalisa ce ta kafa shi don saka ido kan harkokin zabe da kuma bayar da rahoto kan duk wani rashin gaskiya da kuma magudi.

Heikal Kenneded, wani masani dan asalin kasar Somaliya da ke da zama a Virginia, ya ce ya ga masu fafatukar zaben na ta raba kudi lokacin da ya je Mogadishu makon jiya, kodayake ba zai iya bayyana ko su waye ba.

XS
SM
MD
LG