Kamar yadda ake ci gaba da gudanar da yakin zabe a jamhuriyar Nijer, yau shirin yau da gobe cikin a cikin zantawar da yake da jam'iyyun kasar masu 'yan takarar shugaban kasa, ya sami zantawa ne da jam'iyyar MODEN FA LUMANA AFRICA.
Malam Mamman Sani Shine magatakardar jam'iyyar kuma kakakin Hamma Amadou dan takarar shugaban kasar jam'iyyar da gwamnatin Nijer ta jefa a gidan kaso bayan ya koma kasar daga Faransa a ranar 14 ga watan Nuwambar da ya gabata.
Malam Mamman ya bayyana manufofi goma sha hudu na jam'iyyar MODEN LUMANA kamar haka;
Na farko shine gyara tsarin mulki domin shine ke kawo cikasa ga mulkin kasa.
Na biyu shine kulawa da walwalar 'yan adam, da karfafa shi.
Na uku shine samar da hasken wutar lantarki
Akwai kuma amfani da ma'adanai ta hanyar data kamata kamar su uranium, da fetur da hasken rana da sauran su domin inganta rayuwar dan'adam.
Sai kuma harkar neman ilimi da kiwonnlafiyar jikin mutum, lallai gwamnati zata bada kulawa mai muhimmanci akan wadannan.
Akwai bunkasa harkar noma da kiwo, domin babu wani abu da yafi harkar noma da kiwo a kasar Nijer.
Za'a samar da isashshen ruwan sha tun da Nijewr na cikin hamada ne, dan haka jama'a zasu bukaci ruwa mai kyau domin kiwo da noma da sauran su.
Na biye da wannan shine samo masu zuba hannun jari domin taimakawa jama'a ta hanyoyi daban daban kama daga samar da aikin yi zuwa kayan masarufi.
Budewa matasa mata da maza hanyoyin ilimi da kiwon lafiya da kuma ayyukan jarida da sauran su.
Saurari cikakkiyar hirar anan..