A ranar Alhamishin nan jam'iyyar PDP zata gudanarda zaben fitarda gwani na dan takaranta na shugaban kasa tsakanin mutane biyu, wanda zai tsayawa jam'iyyar a zaben da za'ayi a watan Afrilun wannan shekara. Gwabzawar za'ayi tane a tsakanin shugaban kasa maici yanzu Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Alhaji Atiku Abubakar. Rahottani daga Abuja na cewa an dauki tsauraran matakai a Dandalin Eagle dake nan birnin na tarayya inda za'a gudanarda zaben. Daruruwan 'yan jam'iyya ne ake sa ran zasu jefa kuri'unsu a zaben. Kafin zuwa yanzu, aksarin duk gwamnonin PDP sun ce suna goyon bayan Mr. Jonathan, yayinda shi kuma Atiku Abubakar, wanda kuma shine Turakin Adamawa, yake morewa zama dan takaran da yankin Arewancin Nigeria ya tsaida don ya wakilce shi a wannan takara. Duk wanda yayi nasara a zaben fitarda gwanin shine zai fuskanci 'yan takaran sauran jam'iyyu na shugaban kasa a zaben na watan Afrilu.
A ranar Alhamishin nan jam'iyyar PDP zata gudanarda zaben fitarda gwani na dan takaranta na shugaban kasa tsakanin mutane biyu, wanda zai tsayawa jam'iyyar a zaben da za'ayi a watan Afrilun wannan shekara.