Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Da Ke Mulki A Nijeriya Zata Yi Zaben Fidda Kwani Yau


Goodluck Jonathan (la hagu), Atiku Abubakar
Goodluck Jonathan (la hagu), Atiku Abubakar

Yau Alhamis Jam’iyyar da ke mulki a Nijeriya za ta yi zaben fidda dan takaran Shugaban Kasa a zaben da za a gudanar a watan Afirilu.

Yau Alhamis Jam’iyyar da ke mulki a Nijeriya za ta yi zaben fidda dan takaran Shugaban Kasa a zaben da za a gudanar a watan Afirilu.

Shugaba Goodluck Jonathan na fuskantar kalubale daga tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, da kuma wata dadaddiyar ‘yar siyasa Sarah Jibril.

To saidai masu lura da al’amura sun ce kuri’un za su rabu gida biyu ne tsakanin Mr. Jonathan day a fito daga Kudu da kuma Mr. Abubakar day a fito daga Arewa. Sama da biyu bisa ukun gwamnonin da ke jam’iyyar sun nuna goyon bayansu ga Mr. Jonathan.

Bisa wata yarjajjeniyar da ba a rubuce ta ke ba, jam’iyyar PDP mai mulki na da tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu bayan wa’adi biyu

Mr. Jonatahn ya zama Shugaba ne a watan Mayun 2010 bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa ‘Yar’Aduwa wanda ya fito daga Arewa, bayan shekaru uku daga cikin wa’adin karba-karbar mai tsawon shekaru takwas.

XS
SM
MD
LG