Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobarar Siyasa Na Kara Ruruwa A Nigeria


Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali na jam'iyyar SDP dake nufin kwace mulki daga APC
Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali na jam'iyyar SDP dake nufin kwace mulki daga APC

Filin siyasar Nigeria yana cike yake da rikici sanadiyar zabukan fitar da ‘yan takara musamman a jam’iyyar APC mai mulki inda a wurare daban daban ana rigingimu har ma da kisa a Bauchi, misali kana wasu da suka fice daga jam’iyyar adawa ta PDP na buga kirjin shirin kwace gwamnati daga hannun APC

Gobarar siyasar dake ci a na Nigeria yanzu ta na kara ruruwa ganin yadda wasu jigajigan ‘yan siyasa da suka fice daga jam’iyyar PDP suke sukar jam’iyyar APC mai mulki musamman a wannan lokacin da ake yawan rikici a zabukan fitar da ‘yan takarar ita jam’iyyar APC din.

Wadanda suka fice daga PDP na ikirarin sun yi hakan ne da zummar damarar kwace mulki daga hannun shugaba Muhammad Buhari na jam’iyyar APC.

Tsohon mai kakakin jam’iyyar PDP wanda yanzu shi ne shugaban kwamitin taron kasa na jam’iyyar SDP Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali ya bayyana manufofinsu. A cewarsa duk lokacin da kasa ta kama hanyar lalacewa Allah yak an kawo wata hanyar gyara.

Parfessa Alkali yace su da suka fice daga PDP suka kafa jam’iyyar SDP, sun yi hakan ne saboda tabarbarewar abubuwa. Burinsu yace shine gyara dazarar suka kama iko.

Sai dai ministan harkokin matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung ya ce akwai dalilin da ya sa wasu ‘yan siyasa ke adawa da shugaba Buhari. Ya ce laifin Buhari daya ne. “Ana cin abinci a cikin duhu ya je ya haska wuta” A cewarsa ba karamin bashi gwamnatin Buhari ta tarar ba, amma yanzu an rage.har ma an boye wasu kudi wajen ajiya. Babu wanda ya san an boyesu. Ya ce kafa TSA, wato ajiye duk kudaden gwamnati cikin asusu daya ya hana yashe dukiyar jama’a, hakan Mr Dalung ya ci gaba d a cewa, ya hana watanda da kudin gwamnati kamar yadda ake yi da can. Ya ce Buhari ya daura damarar yaki da kowa sai ya mayarwa Nigeria arzikinta da aka wawure.

A saurari rahoton Medina Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG