Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Raba Kayan Zaben Najeriya: Aski Ya Zo Gaban Goshi - INEC


Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu

Yayin da babban zaben Najeriya ke dada gabatowa, Hukumar Zaben Najeriya ta INEC ta ce ta yi nisa da rarraba kayan zabe na rukunin farko

A yayin da babban zaben Najeriya ke kara gabatowa, hukumar zabe ta kasar mai zaman kanta INEC tana cigaba da rarraba kayayyakin zabe a rumfunan da za a gudanar da zabe a duk fadin kasar.

Hukumar ta fara ne da rarraba kayan aiki na yau da kullum da ake kira da non sensitive materials a turance Kamar yadda kakakin hukumar Zainab Aminu Abubakar ta bayyana a zantawar ta da Muryar Amurka

Hajiya Zainab tace a shekarar 2021 ne hukumar zaben INEC ta kara yawan rumfunan zabe sakamakon samun cunkuso da ake yi a wasu rumfuna sai dai duk haka ba a samu mutanen da suka sauya katin su daga rumfunar da suka cushe zuwa sabbin rumfuna ba.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, tsakiya, yana kallon wasu daga cikin kayayyakin zaben (Hoto: Facebook/INEC)
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, tsakiya, yana kallon wasu daga cikin kayayyakin zaben (Hoto: Facebook/INEC)

Ta ce hukumar zabe ta sanar wa masu ruwa da tsaki cewa akwai rumfunan da ba za a gudanar da zabe ba dalili kuwa shine babu mutanen da suka sauya katin su zuwa wadannan rumfuna.

Zainab ta ce akwai mutanen da su ka yi amfani da wannan damar don sauya katin su zuwa wasu rumfunan zabe kuma sabbin sauyin yana nan a shafinsu na Internet don ya zame wa mutanen a matsayin tunin rumfar da zasu gudanar da zabe.

Ta cigaba da cewa hukumar zata gudanar da zaben 25 ga watan Fabrairu da na 11 ga watan Maris na shekarar 2023 ne a rumfunan zabe dubu dari da saba’in da shida da dari shida da sittin da shida (176,666).

Sai dai kuma a duk lokacin da babban zabe ya zo dab-da dab, akan samu cece-kuce da jita-jita dake yaduwa cikin al’umma, musamman ma a yanzu da ake ganin maganar canjin takardun Naira na iya taka wa zaben burki.

Mai magana da yawun hukumar, Zainab Aminu Abubakar, ta bada tabbacin gudanar da zaben kamar yadda hukumar INEC din ta tsara tun farko, ta ce suna sane da matsalar tsaro da ake fuskanta a fadin kasar kuma ta ce hukumar na aikin hadin gwiwa da gamayyar jami’an tsaro don tabbatar da tsaro a lokacin zabe da ma bayan zaben.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00
XS
SM
MD
LG