Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Zababben Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya Yi Tir Da Zanga Zangar PDP Zuwa Hedikwatar INEC


Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar
Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, sun yi takun-saka, game da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da zanga-zangar da shugabannin jam’iyyar adawa suka yi na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na makon jiya.

Atiku, tare da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu da wasu jiga-jigan jam’iyyar yayin wata zanga-zangar da suka yi a hedikwatar hukumar da ke Abuja, sun bayyana zaben shugaban kasa a matsayin shiririta, inda ya kara da cewa akwai shakku kan gaskiyar INEC saboda zargin rashin cikawa alkawurran da ta yi game da amfani da Tsarin Tabbatar da Masu Zabe na Bimodal, BVAS, da watsa sakamakon ta lantarki daga rumfunan zabe zuwa dandalinta da za a iya ganin sakamakon.

Atiku Ya Jagoranci Zanga-Zangar Lumana Zuwa Ofishin Hukumar Zabe
Atiku Ya Jagoranci Zanga-Zangar Lumana Zuwa Ofishin Hukumar Zabe

Sai dai Tinubu bai amince da Atiku kan yadda zaben ya gudana da kuma sakamakon zaben ba, yana mai cewa dan takarar PDP ba shi da damar yin nasara a zaben, don haka ya kamata ya daina haddasa cunkoson ababen hawa a Abuja ta hanyar zanga-zanga. Tinubu ya kalubalanci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya garzaya kotu inda za a saurari kokensa amma ba hedikwatar INEC ba.

Shugabanin jam’iyyar PDP sun mika wata takardar gargadi da kakkausar lafazi ga hukumar zabe ta INEC, domin bayyana rashin jin dadinsu kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Atiku Ya Jagoranci Zanga-Zangar Lumana Zuwa Ofishin Hukumar Zabe
Atiku Ya Jagoranci Zanga-Zangar Lumana Zuwa Ofishin Hukumar Zabe

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, wanda ya jagoranci sauran shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta zuwa hedikwatar INEC, ya mika wasikar wacce kwamishinan kula da wayar da kan masu kada kuri’a, Dakta Festus Okoye, ya karba a madadin shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

A cikin wasikar mai dauke da sa hannun Ayu da sakataren jam’iyyar PDP na kasa Samuel Anyanwu, kuma aka aika wa shugaban INEC, jam’iyyar ta ce ta yanke shawarar fara tattakin na lumana da wasikar zanga-zangar ta tabbatar, bayan tarukan da dama domin yin nazari a kan zaben.

A halin da ake ciki, INEC ta dage cewa ba ta goyon bayan kowace jam’iyya kamar yadda zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya shawarci Atiku da ya mutunta shekarunsa, yana mai cewa zanga-zangar da jam’iyyar PDP ta yi zuwa hedikwatar INEC wani sabon shirme ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG