A yayin da ake ci gaba da kiki-kaka akan yankin da zai karbi shugabancin Najeriya a shekara ta 2023, wani ayarin ‘yan jam’iyyar APC sun soma nemawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo goyon baya, domin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben na 2023 mai zuwa.
Ayarin mai suna “Progressive Consolidation Group” sun ziyarci jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya, inda suka tattauna da gwamnan jihar, Abdullahi Sule, a fadar gwamnati da ke Lafiya.
Shugaban ayarin Dr. Aliyu Kurfi, ya ce sun zabi Osinbajo ya tsaya takara ne saboda kyawawan halayen shugabanci da ya nuna, tun sa’adda aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasa a shekara ta 2015.
“Mun zo ne da muhimmin al’amari ga siyasar kasar nan” kurfi ya fadawa gwamnan. “Muna kan wata fafutuka ne, wadda daya daga cikin dattawanmu ya karfafa ta, wato mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.”
Ya ci gaba da cewa “mun duba bayanai da tarihi na rayuwa da ayukansa, da kuma gwagwarmayar da ya yi a siyasa, mun kuma amince mu yi aiki tare domin tallata bukatar tsayawarsa takarar shugaban kasa.”
A martanin da ya mayar, gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule, ya ce hakika Osinbajo zai haskaka jam’iyyar APC, idan har ya zabi tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Ya shaidawa ayarin cewa ba su da wata damuwa, idan aka yi la’akari da kyawawan halaye da ayuka da kuma dattakon da Osinbajo ya nuna, da kuma irin kima da mutuncin da yake da shi a jam’iyyar APC, da ma ‘yan Najeriya baki daya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar dattawan Arewa ta ke ci gaba da jaddada matsayarta kan rashin goyon bayan tsarin mulkin karba-karba da ake fafutukar yi, domin baiwa kudancin kasar karbar shugabanci a shekarar 2023, bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Tuni kuma da ‘yan kudancin kasar daga dukkan jam’iyyun siyasa, suka cimma matsayar cewa lalle ne a bai wa yankin damar karbar shugabanci, bayan kwashe tsawon shekaru 8 mulkin yana hannun Arewa.
To sai dai dattawan na Arewa na ganin ba bu hujjar tilasta komawar mulki a wani yanki a tsarin dimokaradiyya, da yawan kuri’un jama’a ne kadai ke da karfin yanke hukunci.