Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce mutane kimanin sama da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya raba su da muhallinsu. Ya ce kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya irin su Nijar da Kamaru na taimakon wadanda su ka shiga kasashen. Wasu jami’an gwamnatin Nijeriya kuma da aka dora ma nauyin cata hanyoyin kawo karshen rikicin Boko Haram sun taka rawar gani, amma wasunsu babu abin da su ka yi
Abin da ke damun su shi ne duk makarantunsu sun rufe sun mai da su wuraren zaman ‘yan gudun hijira. Ya ce ko jiya ma mutane wajen 17,000 su ka zo daga Kukawa kuma har yanzu su na kara shigowa. “Ban san ko ‘yan gudun hijira nawa su ka shigo yau ba; saboda a yanzu haka Ina Abuja, mu na mitin da Shugaban Kasa. Hakanan mu ke. Saidai ka ji an kwace Goza, an kwace Bama, an kwace Damasit, an kwace Abadan, an kwace Malam Fatari, an kwace Baga, an kwace Kukawa, an kwace Karaskama, kuma su na fafatukar kwace ……aikin fa kenan; tashin hankali ne kullum” A cewar Gwamna Shettima.
Da abokin aikinmu Ladan Ibrahim Ayawa ya tambaye shi inda aka kwana dangane da batun taimakon da kwanan baya aka ce kasashen Yammacin Duniya za su bayar, sai ya ce a hakikanin gaskiya bai kamata ma ya ce wani abu game da wannan batu ba saboda abu ne da ya shafi gwamnatin tarayya. Ya ce kodayake ba zai so ya rinka maganar da ba ta shafe shi kai tsaye ba, amma dai ya kamata gwamnatin Nijeriya ta hada kai da duk wata kasar da za ta iya taimakonta a sami zaman lafiya.
Ya ce shi ba zai ji tsaron fadin gaskiya game da wannan al’amarin ba. Y ace gashi duk abin da yake fadi sun zama gaskiya saidai sun tabbatar da abubuwa ne nab akin ciki ban a farin ciki ba. Gwamna Shettima y ace ya so ma da gaskiyarsa ba ta tabbata ba, wato fargabar kara mumin al’amuran ya zama ba ta tabbata ba. Y ace an yi ta zaginsa, har ma da wanda y ace masa jahili, sai gashi gaskiyarsa ta tabbata. Y ace yakamata a kau da banbancin siyasa da addini da kuma kabila a hada kai a kawo zaman lafiya.