A baya dai kiran da shugaban kasa Buhari ya yi na ayi zaben sak, ya taka muhimmiyar rawa a zaben shekarar 2015, inda shugaban ke ganin tafiya ba za ta yi armashi ba, muddin ba zaben "sak" aka yi ba .
Zaben "sak" shi ne salon zaben dukkanin 'yan takarar a karkashin jam'iya guda a matakai daba-daban.
Masu lura da al'amura da dama suna kallon wannan salon zabe a matsayin wanda yake watsi da dyba cancanta.
To sai dai kuma yayin da ake kusan cimma wa’adin farko na wadanda ke rike da madafun iko, manazarta da kuma wasu 'yan siyasa na ganin guguwar Sak, ba ta samar da mafita ba, domin a cewarsu guguwar ta debo baragurbin mutane.
Hon.Abdur Razaq Gidado wani kusa na jam’iyar UDP wato United Democratic Party a Taraba,ya ce da wuya tsarin zabe na Sak ya yi tasiri, musamman a matakan jihohi.
Shi ma da yake tsokaci game da batun, shugaban jam’iyar SDP a jihar Adamawa, Mr. Ibrahim Bebeto ya ce 'yan Najeriya a wannan karon, zabi za su yi a tskanin abinda ya kira "sak," ko Sam ko kuma cancanta," domin a cewarsa ko Buhari ba zai ce sak ba!
Tun kafin lokacin soma kamfen, tuni har wasu 'yan siyasa sun soma lika hotuna da gangami, batun da hukumar zabe ta INEC, ta ce ba za ta lamunta ba.
Barrister Kassim Gana Gaidam, kwamishina a hukumar zaben ta jihar Adamawa, ya ce hakan ya saba wa dokar zabe.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum