Bayan an kammala zabukan 28 ga watan Maris da 11 ga watan Afirilu rundunar 'yansandan jihar Rivers ta kama mutane dari daya da hudu da take zarginsu da aikata miyagun laifuka a lokutan zabukan.
Mutanen sun aikata laifukan ne lokacin zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya da na gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi.
DSP Ahmed Kidaya Muhammad kakakin rundunar yace a zabukan da aka yi sun gudanar da bincike a wasu sassa arba'in da daya lamarin da ya kai ga kama wadanda ake zargi da aikata laifuka su dari daya da hudu..
DSP Ahmed yace suna zargin mutanen ne saboda laifuka da suka ci karo da dokokin zabe da kuma wasu dokokin kasa. Wasu cikinsu an kamasu da katunan zabe na din-din-din da ba nasu ba ne. Wasu kuma an kamasu ne da kayan zabe har da takardun kuri'u da akwatunan zabe. Wasu an kamasu ne a lokacin da suke kokarin lalata abubuwan zabe.
DSP Ahmed yace rundunarsu tana cigaba da kara gudanar da bincike domin gabatar da wadanda ake zargin gaban kuliya. Yace da zara sun kammala bincike sun tabbatar cewa sun aikata laifukan za'a gurfanar dasu gaban kotu.
A wani halin kuma jam'iyyar PDP ta zargi jam'iyyar APC da haddasa hargitsi a jihar. To saidai APC ta musanta zargin.
Ga rahoton Lamido Abubakar.