Ma’aikatar lafiya ta kasar ce ta sanar da wannan albishir ta kuma ce za a ba duk wanda ya sanar da hukuma inda aka sami bullar cutar kyautar saifa dubu ashirin.
Za a kuma biya wanda yake dauke da cutar saifa dubu arba’in idan ya kai kanshi ga jami’an jinya cikin sa’oi 24 da tabbatar da kamuwa da cutar.
Ana daukar cutar kurkunu ne ta wajen amfani da ruwa marar tsabta, kuma yana sa kafar mutum ta kumbura ta tsattage ta rika ruwa ta hanashi tafiya ko ina.
Kimanin mutane miliyan uku da dubu dari biyar ne suke kamuwa da cutar kowacce shekara a kasashen Asiya da Afrika shekarun baya, amma yanzu an kusa shawo kan cutar a duniya baki daya.
Kawo yanzu kasar Sudan ta Kudu ce tafi kowacce kasa a duniya yawan masu fama da cutar kurkunu, wurin da rahoto ke nuni da cewa, mutane dari biyar da ashirin da daya suke dauke da cutar, abinda ya kasance kashi casa’in da shida bisa dari na sauran wadanda ke dauke da kwayar cutar a shekarar da ta wuce. An kuma sami mutane kadan dauke da cutar a kasar Chadi da Mali da kuma Ethiopia.