Shugaba John Atta Mills na kasar Ghana yana shirin ganawa da shugaba Barack Obama na Amurka yau alhamis a fadar White House dake nan Washington domin tattaunawar da Ghana ta ce za ta kara karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.
Darektan yada labarai na shugaba Mills, Koku Anyidoho, ya fadawa Muryar Amurka cewa shugabannin biyu zasu tattauna hanyoyin bunkasa ayyukan raya kasa da kuma huldar tattalin arzikin dake tsakaninsu.
Wannan ziyara tana zuwa ‘yan kwanaki kadan a bayan da kasar Ghana ta yi bukukuwan cikar shekaru 55 da samun ‘yancin kai, kuma shekaru 2 a bayan da shugaba Obama ya ziyarci kasar Ghana a ziyararsa ta farko zuwa Afirka a matsayin shugaban kasa.