Ministan Tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Magashi (Mai ritaya) ya ziyar ci garin Monguno domin ganawa da rundunar hadin guiwa dake yunkurin kakkabe 'yan ta'adda a yankin tafkin Chadi ya kunshi sojojin Najeriya da na Chadi.
Ministan Tsaron ya yi wata ganawar sirri da rundunar sojan Najeriya da suka mara masa baya na fiye da sa’o’i uku a garin Monguno da ke jihar Borno.
A lokacin da yake yiwa sojojin hadin gwiwar bayani, Magashi ya ce aikin sojoji da sauran jamai'an tsaro yana da muhimmanci ainun domin ta dalilinsu ne sauran mutane da ake tunkaho da su suke iya gudanar da ayyukansu. Yace aikin sojojin ya hada da kare mutuncin kasar yadda ya kamata, da kuma taimakawa fararen hula wajen maido da doka da oda.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci in mika sakon fatan alkhairi da kuma goyan bayansa gare ku game da irin ayyukan da ku ke yi a wannan shiyar ta arewa maso gabashin kasar nan kuma yana muku fatan nasara na ayyukan da ku ke yi” a cewar Magashi.
Magashi ya ce makasudin ziyartar su shine ganawa su duka da kuma takwarorin su na kasar Chadi domin "ganin inda zamu inganta ayyukan ku, wadanda muka tattauna sosai da shugabannin ku, kuma sun gaya mana irin matsalolin ku, kana zamu taimaka.Fatanmu anan ita ce ,za ku ci gaba da kyawawan ayyukan da ku ke yi".
Ministan Tsaron dai ya bayyana wa sojojin cewa gwamnati Najeriya da jama’arta ba za su manta da mazan jiya wadanda suka kwanta dama ba, sakamakon sadaukar da rayukan su da suka yiwa kasar, kuma tana sane da irin sadaukar da rai da sojojin Chadi su ke yi wajen taimakawa kasarmu.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Facebook Forum