Shugaban kamfanin Oriental Energy Farm, Alhaji Muhammadu Indimi ya ce za su marawa gwamnatin tarayyar Najeriya baya na inganta samar da abinci a kasar.
Alhaji Indimi ya bayyana hakan ne lokacin da su ke rattaba hannu kan wani shiri na noman masara tsakanin sa da jami'ar Ilorin da ke jihar Kwara a garin Maiduguri babban birni jihar Borno, inda ya karbi kadada dubu goma domin soma noman masara da zai taimakawa Najeriya ta samar da ishenshen abinci ga ‘yan kasar.
“Ina goyon bayan rufe kan iyakoki da Najeriya ta yi na hana shigo da kayayyaki da ba’a bukata cikin kasar, wanda wasu kasashe makota suke neman mayar da Najeriya wajan zuba shara” a cewar Alhaji Indimi.
Ya kuma kara da cewa yanzu haka idan kaje kasar Benin zaka ga shinkafa kusan tan miliyan biyar da ake jira a shigo da su cikin Najeriya, da ba’a bukatar su. Kuma suna cewa ba irin wannan shinkafa suke ci ba suna cin ‘yar gida ne.
Alhaji Indimi ya ce yana matukar farin ciki sosai da aka rufe kan iyakokin kasar, inda ya ce kafin wannan yana da kadada dubu talatin a jihar Kogi da yake nomawa a yunkurinsu na taimakawa wajan samar da wadataccen abinci a kasar.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Facebook Forum