Masu gabatar da kara za su ba da shawarar a sake yanke hukunci ga Erik da Lyle Menendez saboda kashe iyayensu da suka yi a shekarar 1989 a gidan iyalinsu na Beverly Hills.
Hakan zai bai wa 'yan uwan damar samun 'yanci bayan shafe shekaru 34 a kurkuku.
Mai gabatar da kara na Los Angeles County, George Gascón, ya sanar a lokacin wani taron manema labarai a ranar Alhamis cewa ofishinsa zai ba da shawarar a yanke musu hukuncin daurin shekaru 50 zuwa rai.
"Na zo ga matsaya inda na yarda cewa, a karkashin doka, sake yanke hukunci ya dace," in ji Gascón. Ya ce wasu mambobin ofishinsa sun soki wannan shawarar.
Masu gabatar da kara za su shigar da karar a ranar Jumma’a, kuma za a iya gudanar da zaman shari’ar gaban alkali cikin wata guda ko fiye da haka.
An yanke wa ‘yan uwan Menendez hukuncin daurin rai da rai ba tare da yiwuwar samun beli ba a shekarar 1996 da aka same su da laifin kashe mahaifinsu wanda hamshakin mai shirya fina-finai ne a Hollywood da mahaifiyarsu.
Dandalin Mu Tattauna