Babban buri na a matsayina na karamar ‘yar kasuwa shine ina da burin zama dila ta kayayyakin mata, ina sararwa maimakon sai a saro nima in sara, mussaman ma ganin yadda kasuwancin ya saukaka ta shafukan sadarwa, inji Hajiya Murja Ahmad Muhammad.
Hajiya Murja, ta ce a yanzu an daina “sa kwai a Kwando daya” domin kuwa a cewarta an daina dogaro kan sana’a guda maimakon haka tana sana’oi ne daidai da lokaci da kuma abinda ake yayi a wannan lokaci.
Ta ce a yanzu dai tana sayar da atamfofi da mayafa, a cikin gidanta gudun zaman banza. Ta ce ta fara sana’ar ne bayan da ta lura da yadda dan uwanta ke saro kaya a kasashen waje yake kuma bada sari, ta ga cewar ba sai tana zaune a kasuwa ne kadai zata yi sana’ar hannu ba.
A yanzu hajiya Murja ta ce ta tara nata jarin, sanan tana fuskantar kalubalen bashi, tunda a yanzu sana’a dole sai da bashi, wanda hakan wata rana kan kawo cikas ga sana’oin mata.
Facebook Forum