Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gudanar Da Atisayen Hadin Kan Sojojin Duniya A Ghana Da Cote D'ivoire


ATISAYEN SOJOJIN DUNIYA TA FLINTLOCK
ATISAYEN SOJOJIN DUNIYA TA FLINTLOCK

A wata Maris din bana ne ake sa ran fara atisayen sojojin duniya na FLINTLOCK da kasar Amurka ke jagoranta a wani mataki na karfafa huldar sojojin kasashen duniya a yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen nahiyar Afrika musamman na yankin Sahel.

Kimanin sojoji 1,300 daga kasashe talatin ne ake sa ran zasu gudanar da atisayen a kasashen Ghana da Cote Divoire.

Kwamandan sashen gudanarwa na musamman na dakarun sojan kasar Ghana Col Willaim Nortey da yake jawabi yayin taron bude kan fara atisayen daga Accra yace "atisayen sojojin duniya na Flintlock 2023 ya baiwa dakarunmu tare da kawayensu damar gudanar da aiki tare domin karfafa tsaro a yankin Sahel dama nahiyar Afrika baki daya."

ATISAYEN SOJOJIN DUNIYA TA FLINTLOCK
ATISAYEN SOJOJIN DUNIYA TA FLINTLOCK

Ya kuma kara da cewa, ba za'a samu nasara akan 'yan ta'adda ba sai dai an samu hadin kai tare da yarda tsakanin kasashen don haka wannan atisayen nada muhimmanci sosai.

ATISAYEN SOJOJIN DUNIYA TA FLINTLOCK
ATISAYEN SOJOJIN DUNIYA TA FLINTLOCK

Shi kuwa mataimakin kwamandan rundunar tsaron Amurka a Afrika Col. Robert Zyla yace"ba nahiyar Afrika kadai ne ta'addanci ke yi wa barazana ba har da wasu kasashen sassan duniya. In aka samu tsaro a nahiyar Afrika ko shakka ba bu, za'a samu cigaba da tsaro a sassan duniya. Atisayen bana ya maida hankali akan matakan da falaren hula zasu dauka musamman ta fannin kiwon lafiya kuma muna aiki tare da kawayen a nahiyar Afrika domin samar da shirye shiryen karfafa tsaro da zaman lafiya ta fannin mata da ma dokokin a tisaye"

Tsohon kwamanda a dakarun soja na kasar Ghana kana mai sharhi bisa harkar tsaro yace wannan atisaye ya taimaka wajen shawo kan wannan matsala ta tsaro a yankin Sahel.

Tun shekara ta 2005 ne dai manyan kasashen duniya karkashin jagorancin kasar Amirka suka assasa wannnan shiri, a wani mataki na karfafa huldar sojojin kasashen duniya a cikin yaki da kungiyoyin yan ta'adda a kasashen nahiyar Afrika musamman na yankin sahel.

Za a gudanar da atisayen bana ne daga ranar daya zuwa ranar goma sha biyar ga watan Maris a kasashen Afrika ta yamma wato Ghana da Cote Divoire.

Saurari rahoton Hamza Adams cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG