Za a fara tattaunawar zaman lafiya kai-tsaye tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da mayakan M23 a babban birnin Angola a ranar 18 ga Maris, in ji fadar shugaban kasar Angola a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Kasar ta Angola wacce ke yankin Kudancin Afirka ta jima tana kokarin shiga tsakani don samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da rage tashin hankali tsakanin DRC da kasar makwabtanta, Rwanda, wadda ake zargi da goyon bayan mayakan ‘yan tawaye masu biyayya ga kabilar Tutsi.
Rwanda ta musanta wadannan zarge-zarge.
Angola ta sanar a ranar Talata cewa za ta yi kokarin shirya wannan tattaunawa kai tsaye.
Gwamnatin Congo ta yi watsi da tattaunawa da M23 a baya-bayan nan, kuma a ranar Talata, ta samu labarin wannan shiri na Angola.
Ba a sami wani tsokaci daga Kinshasa a ranar Laraba ba.
Dandalin Mu Tattauna