Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Yan’tawayen M23 Na Cigaba Da Kai Hare-Hare A Yankin Gabashin Congo


Mayakan M23
Mayakan M23

A ranar Litiinin Majalisar Dinkin Duniya ta ce, 'yan tawayen M23 sun kaddamar da hare hare a yankin Gabashin Congo inda suka yi garkuwa da a kalla mazaje marasa lafiya da wadanda suka jikkata su 130 daga wasu asibitoci biyu a birnin Goma, a makon da ya gabata.

Mayakan M23 sun kai samame a asibitin CBCA da asibitin Heal Africa a dare 28 ga watan Fabrairu, inda suka yi awon gaba da marasa lafiya 116 da wasu su 15 cewar, mai Magana da yawun ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani cikin wata sanarwa.

Ana kyautata zaton mazajen da aka dauke dakarun Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ne ko kuma manbobin wata kungiyar dake marawa gwamnati baya da ake kira Wazalendo.

Shamdasani ta ce, akwai takaici matuka ganin yadda kungiyar mayakan M23 ke sace marasa lafiya daga gadajen asibiti, a hare haren da ake tsara su sau da kafa, a kuma rike su ba tare da basu damar yin magana da kowa ba a wuraren da ba wanda ya sani, inda ta yi kiran da a gaggauta sakin su.

Masu magana da yawun kungiyar mayakan ta M23 Willy Ngoma da Lawrence Kanyuka Kingston basu ce uffan ba a nan take, a lokacin da aka nemi jin ta bakin su.

Kungiyar kabilar Tutsi mai jagorantar kungiyar ta M23 ta yi tattaki har cikin birnin Goma a karshen watan Janairu, kuma tun daga nan ne suka yi nasarar nausawa cikin Gabashin Congo, suka kwace yankuna da samun iko kan muhimman albarkatun karkashin kasa.

Cigaba da nausawar, wadda ta somo a karshen watan Disamba, tuni ta yi muni wajen rincabewar rikici da ya yadu zuwa cikin Congo na irin kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a shekarar 1994, da fadi tashin da ake yi na samun iko kan dimbin albarkatun karkashin kasa a Congo.

Congo da kwararru a Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashen yammaci duk sun zargi Rwanda da mara bayan kungiyar 'yan tawayen.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG