Dr. Mohammed yace za a gudanar da wannan aikin tare da hadin kan kungiyar Direbobi ta Najeriya, NURTW, wadda tuni har ta zabi tasoshin mota guda biyar domin fara gudanar da wannan aikin.
Dr. Mohammed, wanda yake bayyana wannan a lokacin kaddamar da shirin yaki da Polio na watan Yuli a Bwari, yace wannan wani bangare ne na kokarin kawar da bullar sabuwar cutar Polio a yankin babban birnin tarayya nan da watan Disamba. Yace samar da rigakafin a tasoshi yana da muhimmanci a saboda dukkan rahotannin bullar cutar ana samu ne daga mutanen da suka yi kaura zuwa cikin yankinm.