Hukumar wasan kwallon Kwando ta NBA a Amurka, ta tabbatar da dawowa da buga wasanninta a yau Assabar, bayan da ta jingine wasannin a ranaku 3 a jere, domin nuna damuwar ta akan harbin Jacob Blake.
‘Yan sanda sun harbi Blake, bakar fata mai shekaru 29 a ranar Lahadin da ta gabata a Kenosha ta jihar Wisconsin, lamarin da ya haifar da zanga-zanga, ya kuma sabunta fafutukar nan ta rayuwar bakar fata na da muhimmanci.
Kwamishinan hukumar ta NBA Adam Silver da Michele Roberts, Babban daraktan kungiyar ‘yan wasan NBPA, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a, suna cewa an gudanar da wata muhimmiyar tattaunawa tsakanin ‘yan wasan NBA da masu horadda ‘yan wasa da shugabanni kungiyoyi, akan matakai na gaba na bai daya da za’a dauka na goyon bayan yaki da wariyar launin fata da tabbatar da adalci.
Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta NBA tare da ‘yan wasanta “sun amince da dawowa da buga wasanni a ranar Assabar, haka kuma sun amince da kafa hadakar fafutukar adalci da raba-daidai, tare da wakilcin ‘yan wasa, da masu horar da ‘yan wasa da shugabannin kungiyoyi a hadakar.”
Facebook Forum