Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Wadanda Suka Mutu A Harin Las Vegas Ya Kai Akalla 58


‘Yan sanda a Las Vegas ta Jihar Nevada a nan Amurka sun ce wani mutumi ya bude wuta a kan masu halartar wani wasan mawakan Kaboyi cikin daren lahadi, ya kashe mutane akalla 58, ya raunata wasu 515 a harin bindiga mafi muni a tarihin Amurka.

Shugaba Donald Trump ya bayyana wannan harin a zaman na “tsananin rashin Imani.”

Rundunar ‘yan sanda ta birnin Las Vegas ta ce wanda ya kai harin shine Stephen Paddock, daga garin Mesquite a Jihar ta Nevada. Dan bindigar ya bude wu8ta a kan mutane dubu 22 dake halartar wasan mawakan Kaboyi din daga dakinsa dake hawa na 32 a hotel din Mandalay Bay Casino, wanda ke tsallaken hanya daga inda ake gudanar da wannan wasa.

Baturen ‘yan sanda na birnin Las Vegas, Joseph Lombardo, yace zaratan ‘yan sanda na SWAT sun kutsa dakin maharin, inda suka same shi kwance a mace. Yace sun yi Imani Paddock ya kashe kansa. ‘Yan sanda sun kuma samu manyan bindigogi akalla guda 10 a cikin dakin.

A lokacin da yake jawabi ga kasa, shugaba Trump ya gode ma ‘yan sandan Las Vegas saboda sadaukar da kawunansu da kuma matakan da suka dauka cikin gaggawa a lokacin wannan abu da ya kira “mummunan hari” ya kuma ce zai ziyarci birnin jibi laraba.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin wannan harin, tana mai fadin cewa dan bindigar “sojanta” ne wanda ya karbi Musulunci watamnnin da suka shige, amma kuma ba ta bayar da wata shaidar hakan ba.

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya a Amurka, FBI, ta ce a yanzu kam, ta hakkake cewa wannan mutumin “bay a da alaka da wata kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa” amma kuma zata ci gaba da bincike.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG