Gwamnan jihar Taraba, Architect Darius Dickson Isiyaku, yace su ba korar ma’aikata zasu yi ba, a maimakon haka kara daukar ma’akata zasu yi, batun korar Malamai da gwamna Nasiru El-Rufa’i ta yi na cigaba da jawo cece-kuce a fadin kasar.
Da yake jawabi a wajen wani gangamin nuna murna da karramawar da wata kungiyar kwadago ta yi wa gwamnan jihar Taraba, Arc. Darius Dikson Isiyaku, a birnin tarayya Abuja, gwamnan jihar Taraba, yayi shaguben cewa yayin da wasu ke korar malamai, su gwamnatinsu kara daukar malamai 3000 zata yi a jihar.
Gwamnan wanda ke tarbar dandazon ‘yan jam’iyyar PDP da suka zo tayi shi murna, yace ko ba komi ai gwamnatinsu ta PDP, gwamnati ce dake da tausayin talakawa.
To sai dai kuma fa, yayin da gwamnan da magoya bayansan ke farin cikin lambar yabon, tuni wannan batu ya soma samun suka da martani daga wasu ma’aikatan jihar.
Malam Musa wani karamin ma’aikaci ne a jihar da ya nemi a sakaya cikakken sunansa, yace sun yi mamaki ganin cewa karramawar ta zo ne a dai-dai lokacin da wasu ma’aikatan jihar ke bin albashi na watanni.
Domin karin bayani saurari rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.
Facebook Forum