Mai girma Sarkin Muslmin yace yana kalubalantar duk wanda yace Najeriya tana cikin tsaka mai wuya game da zaman lafiya. Sarkin yace ba kowa ne yake kawowa Najeriya barazana ba illa 'yan siyasa da irin kalamunsu domin ko duk irinsu guda ne. Yace kuma su nawa ne idan aka kwatantasu da talakawa dake faman neman abun da zasu ci. Mai Martaba Sarkin Musulmi yace muddin 'yan siyasa basu shiga taitayinsu ba da irin kalamunsu to har kullum su ne zasu cigaba da zama cikin barazana. Babu ruwan talaka bawan Allah.
Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III yace "Masu cewa kasar na cikin mawuyacin hali game da zaman lafiya to ni ina da ra'ayi da ya sha ban ban da masu wannan ra'ayin domin miliyoyin talakawa basu da matsala tsakaninsu. Matsalar dai tana tsakanin 'yan siyasa masu rura wutar rashin zaman lafiya. Wani lokaci ma ji suke yi kamar yanzu yanzu ne kasar zata kama da wuta kuma duk da ba kowa ba ne sai su"
Shi ma mataimakin shugaban kasa Alhaji Namadi Sambo yace duk yadda shugabanni ke son cigaba idan babu zaman lafiya to suna yaudarar kansu ne. Yace "Wajibi ne mu jajirce wajen samarda zaman lafiya da dokokin da zai haifar da soyayya da kauna a tsakaninmu. Ta haka ne kurum za'a iya gina kasa mai inganci".
Shi kuma tsohon shugaban kasa Janaral Muhammed Buhari ga abun da yake cewa "Ya ku mahalarta wannan taron zan maisheku cikin tarihi game da shugabanci wanda har yau banga mutum irin Joseph Tarka ba wanda Kirista ne daga jihar Binuwai amma kuma ya dauko mutum daga jihar arewa maso gabas ya tsayar dashi zabe kuma yayi nasara. Wani abu sai shugabanninmu na farko.
Amma gwamnan jihar Kaduna Alhaji Mukhtari Ramalan da shima yake tofa albarkacin bakinsa ya yabawa kungiyar Izala domin samarda irin wannan taron. Ga abun da yake cewa "Tattaunawa da yin mahawarori shi ne kadai hanyar da za'a samu zaman lafiya"