Shugaban Amurka Barack Obama, ya kira harbe musulmi uku kusa da wani koleji, a jihar Carolina ta arewa dake nan Amurka, da cewa "rashin imani ne mai bakanta rai".
Mr. Obama, a cikin wata sanarwa da ya bayar ya ce, "Bai kamata ba a ce a Amurka an auna kaiwa wani hari saboda asalinsa, ko kamanni, ko saboda addininsa".
Haka shugaban na Amurka ya tabbatar da cewa hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka da ake kira FBI, ta fara bincike kan kisan domin gano ko an karya dokokin gwamnatin tarayya. Hukumar ta FBI tana tallafawa rundunar 'Yansanda dake yankin wajen gudanar da bincike na farko farko.
A cikin wata sanarwa da reshen hukumar FBI dake jihar Carolaina ta aikewa Muriyar Amurka tace, ta fara gudanar da bincike kafada da kafada da rundunar 'Yansandan dangane da wannan kisan, domin ta gano ko akwai dokokin tarayya da aka keta.
Shima da yake magana kan kisan, Atoni Janar Eric Holder, yace "ya kadu kuma yana cike da bakin ciki, saboda wannan "mummunar laifi" da aka aikata cikin wannan mako.
Hukumomi sun gurfunar da wanda ake zargi mai suna Craig Stephen Hicks, da laifin kisan kai. 'Yansanda suka ce sun hakikance rashin jituwa kan wurin ajiye motoci da aka juma ana yi tsakanin makwabtan, shine musabbabin abunda ya kai ga kisan.
Amma mahaifin matan biyu, Mohammed Abu salha, ya fada ranar laraba cewa, ya hakikance cewa kiyayya ce ta janyo kisan. Yace sai da dama maharin ya tunkari 'yarsa da mijinta yayin yana dauke da binidga.
Amurka tana fassara kiyayya a zaman babban laifi, da ya samo asali saboda kyama ko kin jinin mutum saboda launin fata ko asalinsa, ko domin addini, ko kabila, ko inda ya fito, ko saboda irin rayuwarsa, ko kuma wata larura da wanda ko wadanda aka kaiwa harin suke dashi.