Za'a cigaba da fafatawa a sauran wasannin cin kofin zakarun nahiyar Turai UEFA Champions League na shekara 2017/18 a matakin wasan rukuni zagaye na biyu,
Inda kungiyoyi goma sha shida a yau laraba 21/11/2017 zasu kara a tsarin rukuni hudu.
A rukunin (A) kungiyar kwallon kafa ta Basel zata karbi bakuncin Manchester United, sai kuma CSKA Moscow su kara da Benfica.
A rukunin (B) Anderlecht da Bayern Munich, sai Paris Saint-Germain da Celtic, inda a rukunin (C) akwai Qarabag da zasu gwabza da Chelsea, kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta marabci Roma.
A rukunin (D) kuwa Sporting zata barje gumi da Olympiacos sai kuma babban wasan da zai dau hankalin ma'abuta kwallon kafa a duniya wato wasa tsakanin Juventus da Barcelona.
Za'a fara buga wasannin ne tun daga misalin karfe shida na yammaci har zuwa karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi.
Facebook Forum